ð·ððððððððððð ðªðððððððð, ð¬ð ðððððððððððð, ð©ðððððð, ð¯ðððððððð, ðŸððððð, ð·ðððððððð, ð·ððððððððð, ðªðððððððð, ð¹ððððððððð, ð¬ððððððððððð, ð±ððððððððð, ð·ðððð ðšð ðððððð, ð·ððððððððð, ð¬ððððððð, ð¹ðððððððð, ððð ðºðððð-ð·ðððððððð ðšðððððð, ð¯ðððððð . ð¬ðððð ðð ð ðððð: ðððððððððððððð@ððððð.ððð
Monday, July 27, 2026
ME YA SA SAI ÆAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?
Tuesday, July 21, 2026
IDAN KAGA ABU 5 TATTARE DA MACE KO KA AURETA BA ZAKU ZAUNA LAFIYA BA
Wednesday, July 15, 2026
RASHIN SANIN ASALIN DABI'AR MACE TAMKAR HUKUNCIN KISA NE GA NAMIJI
Tuesday, July 7, 2026
MACE TA GARI KUDI BA YA SAYENTA: DARAJA, MUTUNCI, TARBIYYA DA TSORAN ALLAH SU NE TARAKUNAN KAMATA
A rayuwar aure da zamantakewa, akwai wata muhimmiyar gaskiya da ya kamata kowane mutum ya fahimta: ba kyaw ko tarin dukiya ne ke tabbatar da samun mace ta gari ba. Mace mai tsaftar zuciya da kyakkyawar tarbiyya tana neman abin da ya fi Æarfin dukiya; tana neman namiji mai mutunci, girmamawa, tausayi da tsoron Allah.
Namijin da yake ganin cewa kuÉi ko matsayi za su iya tilasta soyayya ya kamata ya sake tunani. Domin dukiya na iya kawo kusanci na Éan lokaci, amma ba za ta iya sayen Æauna ta gaskiya ko girmamawar zuciya ba. Ana iya mallakar abubuwa da kuÉi, amma zuciyar mutum ta na samun nasara ne ta hanyar kyawawan halaye.
Mace ta gari tana daraja namijin da yake da halin kirki, wanda yake kiyaye mutuncinsa, yake girmama ta, kuma yake nuna mata kulawa cikin gaskiya. Ita ba ta kallon abin da yake hannunsa kawai ba, tana kallon irin mutumin da yake a zuciyarsa da kuma yadda yake mu'amala da ita da sauran mutane.
Idan namiji ya rasa tarbiyya, gaskiya da tsoron Allah, ko da kuwa yana da dukiya mai yawa, zai iya samun damar kusantar mace amma ba zai iya samun cikakkiyar amincewa da Æaunar zuciyarta ba. Domin darajar mutum ba ta ta'allaka ne da abin da yake da shi ba, ta na cikin abin da yake kasancewa.
Saboda haka, duk wanda yake fatan samun abokin zama nagari ya fara gina kansa da kyawawan Éabi'u, domin kyakkyawan hali shi ne babban jari a rayuwar aure. Allah Ya azurta mu da abokan zama nagari masu Æauna, fahimta da taimakon juna. Amin. ð€²
✍️ Tuesday: July 7, 2026
Monday, July 6, 2026
YADDA MUTUM ZAI GANE ANA BIBIYARSA A YANAR GIZO-GIZO (INTERNET)
Sunday, July 5, 2026
TAURIN BASHI DA ILLAR DA YAKE HAIFARWA GA KASUWANCI DA MA'AIKATA
Taurin bashi na nufin halin da mutum, kamfani ko Æungiya ke nunawa na Æin biyan bashin da ake binsa a lokacin da aka cimma yarjejeniya ko kuma jinkirta biyan bashi ba tare da wani ingantaccen dalili ba. A wasu lokuta, mai bashi ya na da ikon biyan abin da ake binsa, amma sai ya Æi ko ya ci gaba da ba da uzuri iri-iri. Wannan hali ya na raunana amana tsakanin masu hulÉar kasuwanci, tare da jefa Éangarori da dama cikin matsalolin kuÉi.
Kasuwanci ya na bunÆasa ne bisa ginshiÆan gaskiya, riÆon amana da cika alkawari. Idan taurin bashi ya zama ruwan dare, yana haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci. 'Yan kasuwa da dama sukan kasa sake sayen kaya da ga masana'antu ko dillalai saboda kuÉinsu na hannun masu bashi. Hakan kan janyo Æarancin jari, raguwar ciniki da kuma durÆushewar wasu kasuwanci.
Daya daga cikin manyan illolin taurin bashi shi ne lalacewar kuÉaÉen gudanar da kasuwanci. Idan kuÉin da ake sa ran za a karÉa sun makale a hannun masu bashi, mai kasuwa zai fuskanci matsalar biyan kuÉin haya, haraji, sufuri, wutar lantarki da sauran kuÉaÉen gudanarwa. Wannan na iya tilasta masa rufe shagonsa ko rage ayyukan kasuwancinsa.
Haka kuma, taurin bashi yana shafar ma'aikata kai tsaye. Idan kasuwanci ya shiga matsin kuÉi saboda rashin karÉo bashinsa, Éankasuwa kan kasa biyan albashi a kan lokaci wa ma'aikatansa. A wasu lokuta kuma, ana rage albashi, ana dakatar da Éaukar sabbin ma'aikata, ko ma a sallami wasu domin rage kashe kuÉi. Wannan ya na Æara yawan marasa aikin yi tare da jefa iyalai cikin Æuncin rayuwa.
Bugu da Æari, taurin bashi ya na rage yawan zuba jari. Masu zuba jari da cibiyoyin kuÉi kan yi shakkar saka hannun jari a wuraren da ake fama da rashin biyan bashi, saboda tsoron asarar kuÉinsu. Wannan na rage ci gaban tattalin arziki tare da hana bunÆasar sababbin sana'o'i da masana'antu.
Har ila yau, wannan hali ya na haifar da rashin yarda tsakanin mutane. Dankasuwa da ya sha asarar bashi kan daina yarda da sababbin kwastomomi ko kuma ya daina sayar da kaya a bashi. Hakan yana takaita damar kasuwanci da kuma rage sauÆin gudanar da mu'amala a cikin al'umma.
A mahangar addinin Musulunci, biyan bashi wani muhimmin hakki ne. Musulunci ya Æarfafa mutane su cika alkawari kuma su biya bashin da ke kansu idan lokacin biya ya yi. Wanda yake da ikon biya amma ya Æi, ya aikata abin da addini ya yi hani a kansa, domin hakan zalunci ne ga mai bin bashi.
HANYOYIN MAGANCE TAURIN BASHI
- A rubuta yarjejeniyar bashi a sarari tare da kaiyade lokacin biya.
- A binciki amincin wanda za a ba bashi kafin a yi mu'amalar da shi.
- A riÆa tunasar da masu bashi cikin ladabi kafin lokacin biya ya Æare.
- A yi amfani da hanyoyin sulhu da doka idan an gaza cimma matsaya.
- A Æarfafa tarbiyyar gaskiya, riÆon amana da tsoron Allah a cikin al'umma.
- Yankasuwa su guji bayar da bashi ba tare da wani tsari ko tabbaci ba.
Taurin bashi wata babbar matsala ce da ke raunana kasuwanci, ta na jefa ma'aikata cikin Æalubale, tana rage zuba jari, tare da kawo cikas ga bunÆasar tattalin arzikin al'umma. Don haka, ya zama wajibi ga kowane mutum ya Éauki biyan bashi a matsayin nauyi da amanar da ya rataya a wuyansa. Idan aka rungumi gaskiya da cika alkawari, za a samu ingantaccen kasuwanci, bunÆasar tattalin arziki da zaman lafiya a tsakanin al'umma.
✍️ Uncle Yunus
Monday: July 6, 2026.
Wednesday, July 1, 2026
GWAMNATIN TARAYYA TA SOKE TSARIN JSS DA SSS, TA GABATAR DA SABON TSARIN ILIMI NA SHEKARU GOMA SHA BIYU (12 YEARS)
SABON TSARIN WHATSAPP: YADDA ZA KA YI AMFANI DA USERNAME MAIMAKON LAMBAR WAYA
MUHIMMANCIN SHAN RUWA DA SAFE BAYAN TASHI DAGA BARCI
Thursday, June 25, 2026
ADVICE TO SECONDARY SCHOOL LEAVERS BEFORE PROCEEDING TO THE UNIVERSITY
UNCLE DANBABA: A DEDICATED EDUCATOR, MENTOR AND NATION BUILDERUncle Danbaba
UNCLE DANBABA: A DEDICATED EDUCATOR, MENTOR AND NATION BUILDER
Wednesday, June 24, 2026
ABUBUWAN DA ZA SU KYAUTATA RAYUWAR MUSULMI
Tuesday, June 23, 2026
MATSAYAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA A MUSULUNCI
Saturday, June 20, 2026
FA'IDODI GUDA GOMA NA TUFA (APPLE) GA LAFIYAR JIKI
Wednesday, June 10, 2026
A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)
Saturday, December 27, 2025
MU TASHI MU TSARE MAKOMAR MU A 2027
Saturday, December 20, 2025
BIKIN SAUÆA: AL'ADACE WASU LOKUTAN DA KE JAWO LALACEWAR TARBIYYAR 'YA'YA MATA
THE RULING ON THE EVIL EYE IN ISLAM
Sunday, December 14, 2025
ð ðððð "ððððððð" ððððððð ðð ðððððð ðð ðððð ðð ð ðððð ð ððð ððððð ððððð ðð ððððð ðð ðððð-ðððð ððÆðÆðð ðððððð ðð ððð ðððð ðð.
ME YA SA SAI ÆAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?
Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Æauna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Éaci wacce bama son faÉa sabi...
-
Assalamu alaikum. HaÆiÆa, wani mummunan yanayi da ya kamata ya girgiza zukatanmu a matsayin al’umma, musamman iyaye, malamai da ...
-
Aure ginshiÆi ne na rayuwa, kuma yana daga cikin manyan al'amuran da ke buÆatar zurfin tunani da bincike kafin a yanke hukun...
-
Rayuwar aure da zamantakewa ba ta ta'allaka ne da soyayya kaÉai ba, tana buÆatar fahimta, haÆuri da sanin dabi'un juna. Namijin da b...