Saturday, December 27, 2025

MU TASHI MU TSARE MAKOMAR MU A 2027


Ya ku Musulman Najeriya! Lokaci ya yi da za mu farka mu gane abin da ke faruwa a ฦ™asarmu. Abin takaici ne yadda aka kai hari a Arewacin Najeriya, musamman a Jihar Sokoto, waima da sanin gwamnati. Wannan al’amari ya taษ“a martabar ฦ™asarmu Najeriya, addininmu na Musulunci, ya kuma ragewa Najeriya daraja a idon duniya kwarai da gaske.

Ku sani, tarihi ya tabbatar mana da cewa Sokoto ba jiha ba ce kawai; tana da tarihi mai girma na Daular Musulunci ta Usmaniyya. Duk wani abu da ya shafi tsaron wannan yanki yana da muhimmanci ฦ™warai da gaske, kuma ya kamata shugabanci ya tsaya tsayin daka wajen kare mutunci da ‘yancin ฦ™asa, ba yawuce gaba ba don tozartata idon duniya l.

Idan shugabanci bai iya kare rayukan jama’a da martabar ฦ™asa ba, to ya zama wajibi a tambayi sahihancinsa. Shiru ko sakaci a irin wannan lokaci alama ce ta gazawa, kuma gazawa ba ta cancanci ฦ™arin dama ba ga kowane irin shugaba da yake riฦ™e da madafin iko ba.

Saboda haka, ya zama wajibi ga duk ษ—an Arewa, musamman Musulmi, ya fahimci cewa Tinubu da duk masu mara masa baya ba su cancanci sake ba su shugabancin Najeriya ba a 2027. Ba za su iya kare addininmu ba, imanimmu ba, ฦ™asarmu ba, ballantana makomar ‘ya’yanmu; abin da ya dame su shi ne jin daษ—in kansu da na iyalansu.

Mu farka daga dogon baccin da muke yi. Mu haษ—a kai, mu yi amfani da kuri’armu a matsayin makami na halal, tare da kai ฦ™orafinmu ga Allah SWT. Shi ne mafi adalci, kuma Shi kaษ—ai ne zai yi mana hukunci bisa gaskiya. Idan kunne ya ji, to shakka babu jiki ya tsira.
✍️ Yunus Historian Hadejia

No comments:

Post a Comment

MU TASHI MU TSARE MAKOMAR MU A 2027

Ya ku Musulman Najeriya! Lokaci ya yi da za mu farka mu gane abin da ke faruwa a ฦ™asarmu. Abin takaici ne yadda aka kai hari a Arewacin Naje...