Saturday, December 20, 2025

BIKIN SAUƘA: AL'ADACE WASU LOKUTAN DA KE JAWO LALACEWAR TARBIYYAR 'YA'YA MATA

Assalamu alaikum.

HaΖ™iΖ™a, wani mummunan yanayi da ya kamata ya girgiza zukatanmu a matsayin al’umma, musamman iyaye, malamai da shugabannin addini. Abin takaici ne yadda abin da ya kamata ya zama ibada da godiya ga Allah ya koma sanadin lalacewar tarbiyya.

SauΖ™a a Musulunci ibada ce, ba gasa ba ce, ba kuma wajibi ba ne a yi walima mai tsada. Amma yau an juya ta zuwa al’ada mai matsin lamba, wadda ke jefa wasu Ι—alibai cikin halin kunci da tsanani.

Abin tausayi ne yadda wasu ‘ya’ya mata ke shiga hanyoyin da ba su dace ba domin kawai a samu kuΙ—in walima. Wannan ba laifinsu kaΙ—ai ba ne, laifin tsarin da ya Ι—ora musu nauyi fiye da Ζ™arfinsu ne.

Wasu kuma suna shirya Ζ™arya, yin rancen da ba za su iya biya ba, ko yin yandabaru dabaru marasa kyau, duk saboda tsoron abin da mutane za su ce idan ba a yi walimar ba.

Ya kamata mu gane cewa duk wata al’ada da ke haifar da lalacewar Ι—abi’a, to dole ne a dakatar da ita ko a gyara ta. Addini bai taΙ“a goyon bayan abin da ke kai mutum ga zunubi ba.

Shawara ga ‘yan’uwa mata: ku sani cewa darajarku tana cikin tarbiyya da tsoron Allah, ba cikin girman walima ba. Allah bai Ι—ora muku abin da ba za ku iya ba.

Shawara ga iyaye: ku rage matsin lamba, ku yarda da sauΖ™a ko da ba a yi walima ba. Ku kare ‘ya’yanku daga shiga hanyoyin da za su lalata rayuwarsu gaba Ι—aya.

Shawara ga malamai da shugabanni: lokaci ya yi da za a fito a faΙ—i gaskiya a fili cewa walimar sauΖ™a ba wajibi ba ce, kuma a soki duk wani tsari da ke haddasa fasadi.

Mafi alheri shi ne a sauΖ™a a cikin nutsuwa, a yi godiya ga Allah, a yi addu’a, ko da ba tare da taro, kiΙ—a ko ciyarwa ba. Wannan shi ne ainihin ruhin ibada.

Don haka, idan walimar sauΖ™a ta zama sanadin lalacewa, to sokewa ko takaita ta ya fi zama alheri. Allah ba ya karΙ“ar ibadar da aka gina ta kan cutar da bayinsa.

✍️ Uncle Yunus
Saturday: December 20, 2025.

No comments:

Post a Comment

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabi...