Wednesday, June 10, 2026

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ฦ™ai, muna ci gaba da miฦ™a komai ga Allah SWT tare da addu’ar Ya jiฦ™an ษ—anmu RAYYAN, Ya yalwata masa rahama da gafara, Ya sanya kabarinsa ya zama lambun Aljanna. Muna roฦ™on Allah Maษ—aukakin Sarki Ya sa maceci ne ranar alฦ™iyama.

Ina miฦ™a godiya ta musamman ga ษ—aukacin al’umma bisa irin tsayuwar da kuka yi tare da mu a wannan lokaci na alhini. Haฦ™iฦ™a mun ga soyayya, tausayi, jajantawa da addu’o’i daga gare ku ta hanyoyi masu yawa. Allah SWT Ya saka muku da mafificin alkhairi, Ya albarkaci rayuwarku da iyalanku, Ya kuma jiฦ™an naku waษ—anda suka riga mu gidan gaskiya.

Muna ฦ™ara roฦ™on Allah SWT Ya sanya mu da ku cikin masu riฦ™o da Sallah, imani da kyawawan ayyuka har zuwa ฦ™arshen rayuwa. Mu da muka rage, Allah Ya sa idan lokacinmu ya yi, mu tafi cikin kyakkyawan ฦ™arshe da cikar imani. Allah Ya haษ—a mu da Rayyan a Aljannatul Firdausi. Amin Ya Rabbal Alamin.

✍️  Abbun Rayyan - Yunus Historian Hadejia 
Wednesday: June 10, 2026 - Dhul-Hijjah 20, 1447 AH.

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN) Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ฦ™ai, muna ci gaba da miฦ™a ko...