Tuesday, June 23, 2026

MATSAYAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA A MUSULUNCI

Azumin Tasu'a (rana ta 9 ga Muharram) da Ashura (rana ta 10 ga  Muharram) suna daga cikin manyan sunnonin da Manzon Allah ๏ทบ ya koyar. Lokacin da ya isa Madina, ya tarar Yahudawa su na azumin ranar Ashura (10) saboda ranarce da Allah Ya ceci Annabi Musa (AS) da mutanensa daga Fir'auna. Sai Manzon Allah ๏ทบ ya ce: "Mu ne mafi cancanta ga Musa fiye da ku," sannan ya yi azumin ranar kuma ya umurci Musulmi da su yi.

Dangane da azumin Tasu'a (9) kuwa, Manzon Allah ๏ทบ ya baiyana cewa: "Idan na rayu zuwa shekara mai zuwa, zan yi azumin ranar tara." Malamai su ka ce hakan yana nuna falalar haษ—a ranar tara da ta goma wajen azumi domin bambanta Musulmi da Yahudawa. Saboda haka, mafi falala shi ne a yi azumin Tasu'a da Ashura tare.

Babbar falalar azumin Ashura ita ce abin da Manzon Allah ๏ทบ ya faษ—a cewa yana zama kaffarar ฦ™ananan zunuban shekara guda da ta gabata, da yardar Allah. Wannan falala ce mai girma da ya kamata Musulmai su yi ฦ™oฦ™arin samu ta hanyar raya wannan sunnah mai albarka.

A bisa lissafin watan Muharram na wannan shekara 1448 A.H, gobe Laraba ita ce 9 ga Muharram (Tasu'a), yayin da jibi Alhamis ce 10 ga Muharram (Ashura). Don haka, wanda yake son samun falalar Tasu'a zai yi niyyar azumi tun daga daren yau Talata, ya wayi gari da azumin ranar Laraba 9 ga Muharram. Haka kuma, zai sake yin niyyar azumin Ashura a daren Laraba, ya wayi gari da shi ranar Alhamis 10 ga Muharram.

Saboda haka, Musulmai su yi amfani da wannan dama mai albarka ta azumin ranar Laraba (Tasu'a) da Alhamis (Ashura) domin neman gafarar Allah, ฦ™arin lada da kuma koyi da Sunnah ta Manzon Allah ๏ทบ. Allah Ya karษ“i ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sa mu kasance cikin bayinsa na ฦ™warai. Amin Ya Rabbal Alamin. ๐Ÿคฒ๐Ÿป

✍️ Uncle Yunus
Talata: 8th Muharram, 1448 A.H - June 23, 2026.

No comments:

Post a Comment

MATSAYAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA A MUSULUNCI

Azumin Tasu'a (rana ta 9 ga Muharram) da Ashura (rana ta 10 ga  Muharram) suna daga cikin manyan sunnonin da Manzon Allah ๏ทบ ...