Wednesday, June 24, 2026

ABUBUWAN DA ZA SU KYAUTATA RAYUWAR MUSULMI

A rayuwa, akwai mutane da yawa da bai kamata mu raina su ba ko kaΙ—an don kawai basu kaimu ba ko sun kasa ta wasu bangarori. Maraya, miskini, mace, marar lafiya da talaka duk suna da daraja a wurin Allah. Idan watarana su na cikin wani hali, wata rana kuma Allah SWT na iya Ι—aukaka su fiye da yadda ake zato.

Haka nan, ka da mutum ya raina iyayensa, ‘yan’uwansa ko matarsa, ko kuma wasu mutane da alokacin shi ba kowa bane sun taimake shi. Su ne mafi kusancin mutane gare shi, kuma kyakkyawar mu’amala da su ta na kawo albarka, soyayya da kwanciyar hankali a rayuwa da samun natsuwar zuciya matuΖ™a.

Babu shakka, Musulmi ya kamata ya nisanci hassada, fushi, girman kai da rudu da Ζ™asaita. WaΙ—annan Ι—abi’u su na haifar da saΙ“ani, Ζ™iyayya da zubewar mutuncin mutum a duniya da lahira.

Har ila yau, ka da a yi wasa da dangantaka da Allah, addini, son Manzon Allah ο·Ί da kuma aikibda dukkan abinda ya umarta. WaΙ—annan su ne ginshiΖ™an rayuwa maibcike da albarka da nasara.

A Ζ™arshe, ka da a yi wasa da sallah, karatun AlΖ™ur’ani, zikiri da zumunci. Dorewa a kansu ya na Ζ™ara kusanci ga Allah, ya na kawo natsuwa ga zuciya, kuma ya na gina kyakkyawar al’umma mai haΙ—in kai da zaman lafiya. Allah SWT ya wuce mana gaba a duk inda muka kasance, Allahumma amin 🀲.

✍️ Uncle Yunus
Laraba: June 25, 2026

No comments:

Post a Comment

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabi...