Monday, July 27, 2026

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabida kusan dukanmu muna aikata wannan Ι—abi'ar sau da yawa.

Mamaci na raye, ya nemi ka ba shi ₦2,000 domin magani ko abinci, sai ka ce, "Wallahi babu kuΙ—i, rayuwa ta yi tsada." Amma ranar da ya rasu, cikin Ζ™anΖ™anin lokaci za ka iya kashe ₦50,000 ko fiye wajen sayen likkafani, shirya abincin ta'aziyya da sauran hidimomi. Ka tambayi kanka: me ya sa ba ka taimaka masa lokacin da yake cikin buΖ™ata ba, sai bayan ya daina buΖ™atar komai inba addu'a ba.

Haka nan, ya na Ζ™iran ka a waya amma ba ka Ι—auka. WataΖ™ila ka ce, "Zan kira shi anjima," amma anjimar ba ta taΙ“a zuwa ba. Sai dai ranar da aka sanar da rasuwarsa, za ka kashe kuΙ—i wajen sayen data domin cika WhatsApp Status, Facebook groups da Instagram da hotunansa, kana rubuta kalaman alhini. Amma gaskiyar magana ita ce, mamaci ba ya kallon WhatsApp Status, Facebook, Instagram da sauransu. Lokacin da yake buΖ™atar taimakonka da jin muryarka, ka Ζ™i kuma ka yi shiru.

Ya na raye ba ka taΙ“a gaya masa cewa kana alfahari da shi ko kana Ζ™aunarsa ba. Amma a ranar jana'izarsa, ka na yabonsa kana cewa wane mutumin kirki ne, ya na da kaza-da-kaza na kyawawan halayesa. To me zai hana ka riΖ™a taimaka masa duk lokacin da yake da buΖ™atar taimakonka da faΙ—in waΙ—annan kalmomi tun ya na raye domin ya ji daΙ—in su?

Mu daina abin da za a kira "Soyayyar Kabari." Idan kana son mutum, ka bari aikinka ya gaya masa yanzu. Idan kana da abin da zai taimaka masa, ka ba shi yanzu tun yana numfashi. Wallahi, buhu guda Ι—aya na shinkafa da za ka ba shi yau ya ci ya Ζ™oshi ya fi shanu biyar da za a yanka ranar mutuwarsa.

Kada ka jira sai hotonsa ya zama na RIP a WhatsApp, Facebook, Instagram, Telegram, Tiktok sannan ka gane darajarsa. Kyautatawa ita ce mafi dacewa da amfani idan an yi ta ga mai rai, domin shi ne zai amfana da ita tun kafin ya rasu.

Ya Allah, Ka yafe mana kura-kuranmu, Ka ba mu ikon kyautata wa iyaye, 'yan'uwa, abokai da maΖ™wabta tun suna raye. Kada Ka sa mu fifita darajarsu bayan sun rasu fiye da su na raye. Amin Ya Rabbal 'Alamin.

✍️ Historian Hadejia 
Monday: July 27, 2026.

No comments:

Post a Comment

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabi...