Wednesday, June 10, 2026

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)

A YAU NE MU KE YIN ADDU'AR UKUN MARIGAYI MUHAMMAD YUNUS MUHAMMAD (RAYYAN)

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Ζ™ai, muna ci gaba da miΖ™a komai ga Allah SWT tare da addu’ar Ya jiΖ™an Ι—anmu RAYYAN, Ya yalwata masa rahama da gafara, Ya sanya kabarinsa ya zama lambun Aljanna. Muna roΖ™on Allah MaΙ—aukakin Sarki Ya sa maceci ne ranar alΖ™iyama.

Ina miΖ™a godiya ta musamman ga Ι—aukacin al’umma bisa irin tsayuwar da kuka yi tare da mu a wannan lokaci na alhini. HaΖ™iΖ™a mun ga soyayya, tausayi, jajantawa da addu’o’i daga gare ku ta hanyoyi masu yawa. Allah SWT Ya saka muku da mafificin alkhairi, Ya albarkaci rayuwarku da iyalanku, Ya kuma jiΖ™an naku waΙ—anda suka riga mu gidan gaskiya.

Muna Ζ™ara roΖ™on Allah SWT Ya sanya mu da ku cikin masu riΖ™o da Sallah, imani da kyawawan ayyuka har zuwa Ζ™arshen rayuwa. Mu da muka rage, Allah Ya sa idan lokacinmu ya yi, mu tafi cikin kyakkyawan Ζ™arshe da cikar imani. Allah Ya haΙ—a mu da Rayyan a Aljannatul Firdausi. Amin Ya Rabbal Alamin.

✍️  Abbun Rayyan - Yunus Historian Hadejia 
Wednesday: June 10, 2026 - Dhul-Hijjah 20, 1447 AH.

No comments:

Post a Comment

IDAN KAGA ABU 5 TATTARE DA MACE KO KA AURETA BA ZAKU ZAUNA LAFIYA BA

Aure ginshiΖ™i ne na rayuwa, kuma yana daga cikin manyan al'amuran da ke buΖ™atar zurfin tunani da bincike kafin a yanke hukun...