Wednesday, July 1, 2026

MUHIMMANCIN SHAN RUWA DA SAFE BAYAN TASHI DAGA BARCI

Shan ruwa bayan tashi daga barci na daga cikin kyawawan Ι—abiu da ke taimakawa lafiyar jiki. Bayan mutum ya kwashe sa'o'i yana barci ba tare da ya sha ruwa ba, jiki kan rasa wani Ι“angare na ruwan da yake buΖ™ata. Shan ruwa da safe yana taimakawa wajen mayar da wannan ruwa cikin jiki.

Haka kuma, shan ruwa da safe na taimakawa wajen inganta narkewar abinci, sauΖ™aΖ™a fitar da bayan gida, da kuma taimakawa Ζ™oda wajen tace datti daga jiki. Ya na kuma taimakawa fata ta kasance cikin Ζ™oshin lafiya da kuma rage jin gajiya ko kasala da wasu ke ji bayan sun tashi daga barci.

Abu mafi muhimmanci shi ne mutum ya tabbatar yana shan isasshen ruwa a tsawon yini gwargwadon buΖ™atar jikinsa. Ka da ya manta da shan ruwan da safe yayin tashi daga barci a kullum Allah SWT ya tashe mu.

Domin samun ingantacciyar lafiya, ya na da kyau a fara da a cup of glass of water, sannan a ci gaba da shan ruwa akai-akai tare da cin abinci mai gina jiki da gudanar da rayuwa mai lafiya. Allah SWT ya Ζ™ara mana lafiya ta amfanar da mu duniy da lahira. Allahumma amin. 

✍️ Uncle Yunus 
Wednesday: July 1, 2026

No comments:

Post a Comment

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabi...