Wednesday, July 1, 2026

SABON TSARIN WHATSAPP: YADDA ZA KA YI AMFANI DA USERNAME MAIMAKON LAMBAR WAYA


WhatsApp ya fara Ζ™addamar da sabon tsarin Username, wanda zai ba masu amfani da shi damar yin hulΙ—a da junansu ta hanyar amfani da suna (username) maimakon bayar da lambar wayarsu kai tsaye. Wannan sabuwar fasahar zata Ζ™ara kare sirri tare da sauΖ™aΖ™a hanyar sadarwa tsakanin masu amfani.

Domin amfani da wannan tsarin, da farko ka tabbatar ka sabunta (Update) manhajar WhatsApp Ι—inka ta hanyar Google Play Store ko Apple App Store. Bayan haka, shiga Settings → Account → Username.

A wajen Username, rubuta sunan da kake so a matsayin username Ι—inka. Idan wani ya riga ya mallaki shi, za a buΖ™aci ka canza shi ko ka Ζ™ara wasu lambobi ko haruffa domin ya zama na musamman. Bayan ka kammala, danna Save domin adana username Ι—inka.

Da zarar an adana username Ι—inka, za ka iya raba shi ga mutane domin su same ka cikin sauΖ™i ba tare da ka ba su lambar wayarka ba, abin da zai taimaka wajen Ζ™ara kare sirrinka yayin amfani da WhatsApp. Ku daure ku yi tun kafin wani ko wata su riga ka Ι—aukar irin username Ι—in da kake son yin amfani da shi. 

✍️ Uncle Yunus 
Wednesday: July 1, 2026.

No comments:

Post a Comment

ME YA SA SAI ƊAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?

Wallahi, muna rayuwa ne a wani zamani da ake yawan nuna wa mamaci Ζ™auna fiye da mai rai. Wannan gaskiya ce mai Ι—aci wacce bama son faΙ—a sabi...