1. Kayi iya yinka wajen gujewa bashi, sai in ya zama dole, kuma da zarar ka samu sukunin biya to kayi hakan da wurwuri. "Bashi ba karamar barazana bace ga cigaba"
2. Idan Allah ya hore maka aiki ko sana'a, ka dinga aje wani kaso komai ฦarancinsa, a asusun ajiyarka. "Ajiya maganin wata rana"
3. Aฦalla ka samu abin yi fiye da ษaya, "Gida biyu maganin gobara"
4. A kowace safiya kamin rana ta faษi, yi ฦoฦari ka iya wani sabon abu. Wayar da kake riฦewa makaranta ce babba "Ilmi kogi ne"
5. Aฦalla kowane mako ษaya, ka yi ฦoฦarin karanta wani littafi. Akwai darussa da dama ฦunshe acikin littafai. "Ilmi haske"
6. Ka dinga motsa jiki aฦalla sa'a ษaya a rana. " mafi yawan ciwarwata/cututtuka nada alaฦa da rashin motsa jiki.
7. Ahir, kashe dinka da zaman majalisa, amadadin haka yi wani abin da zai amfaneka da wannan lokaci, ko dai koyon wani abu ko neman ilmi. "Zaman kashe wando illa ce babba, kuma hurumi ne na wanzuwar giba da annamimanci" Ba zaka gane muhimmancin lokaci ba sai girma ya sameka.
8. Ka dinga tashi tunda safe domin tunkarar ayukan ka na wannan rana. "Da sassafe ake kama fara"
9. Kowane yini kamin rana ta faษi, yi ฦoฦari ka taimaki wani, ko da sadaka koda shawara kai koda da baiwa ฦadangaru ruwan sha ne. "Kar ka manta, wata karuwa ta samu gafarar Allah sakamakon yin taimako irin wannan"
10. Tallafi iyayenka da komai ฦanฦantar abin da Allah ya hore maka, ko da kuwa suna da sukuni. "Akwai albaka sosai a taimakawa iyaye da yi masu biyayya"
✍️ Uncle Yunus
No comments:
Post a Comment