Duk maison buΙe whatsapp accounts biyu akan wayar sa/ta ta Android Smartphone ya shiga whatsapp Ιinsa, ya duba daga sama, Ιangaren dama ya danna Ιugo uku-ukunnan da ke asama, sai ya shiga "setting" zaiga "Account", to ananne zai ga "Add Account" sai ya shiga domin Ζara wani whatsapp account Ιin, ammafa shi whatsapp account Ιin na biyu da zai buΙe, ya sani da wata lambar wayar zai buΙe shi, kunga whatsapp accounts Ιinsa ya zama biyu kenan akan waya Ιaya.
Sabida haka, da zarar ya na son yin amfani da whatsapp dinsa, idan ya buΙe shi, sai ya koma kan wannan Ιugo uku-ukunnan ya shiga, yana shiga zaiga aΖasan setting ansa "Switch accounts" to ananne zai riΖa sanja duk whatsapp account Ιin da ya ga damar yin amfani da shi kamar yadda nima haka nake yi. Ammafa, ku sani cewa wannan damace ga masu amfani da normal whatsapp kawai, ba su bada ita ga masu amfani da whatsapp business account ba.
Allah SWT Ya sa muyi amfani da shi ta yadda ya dace. Nagode. Allah SWT ya mana albarka π€².
© Uncle Yunus
No comments:
Post a Comment