Assalamu alaikum...
Cikin jimami da hakan ya sha faruwa ga mutane masu ษinbin yawa, hadda ma manyan mutane, kuma yanzu wannan damfara - 419 tana ฦaruwa musamman ma ta yanar gizo-gizo.
Wannan sabuwar damfara - 419 ษin itace: ana samun wasu marasa tsoran Allah SWT suna hacking - kwace facebook account ษin mutane, musamman ma mashahurai ta bangarori da yawa, suna tallata hajar su ga mutane cewa, ga wani sabon hannun jari, kasa ฦudi dubu N30,000.00 zuwa sama, za ka sami ninkin abinda ka sa cikin ฦasa da minti arba'in (40minutes), suna sanya wani WhatsApp link ษin ne, su ce wanda ya ke son shiga tsarin to ya danna wannan WhatsApp link ษin...
Babu shakka, a sakamakon suna hacking - ฦwace facebook account ษin sanannun mutane, kuma suyi amfani da shi wajen yaษa wannan damfarar - 419 yasa da yawan zarmammun mutane ke yarda har su biye musu, su shiga ta wannan Whatsapp Link ษin da suke ษorawa domin damfarar mutane su sanya hannun jarin su kamar yadda suke yaudarar su domin samun ninkin abinda mutum ya sanya.
Sukan yi hakanne ta hanyar tambayar mutun, da nawa zai fara? N30K, ka sami N60K, ko kuma N50K = N100K, N150K =N300K zuwa sama, ya danganta da irin zarmewar ka. Suna ฦara bada misali da amfani da wasu facebok accounts ษin cewa suma sun samu harma su nuna maka transaction receipt ษin bogi, domin ฦara yaudarar mutune su kuma gaskata tsarin, alhali ฦaryane, damfarane, yaudara ce.
Da yawan mutane sun tura musu kuษaษen su da nufin sanya hannun jari amma shiru ka ke ji, ba labari, idan ka tuntube su, ya naji shiru? Sai su ce sun tura ma amma network ya canja tsarin da ka cike na farko, yanzu sai ka ฦara wani kuษin sannan za ka iya samun ninkin duk kuษin da ka sanya alhali duk damfarane - 419. Idan kai zarmamme ne sai ka sake tura musu, za su ci gaba da yin hakan ga reka har sai sun tatse ka sai su barka hakanan, ba uwar kuษi ba riba.
Kaima, nima maiyuwa munsan wanda aka taba hacking- sace/ฦwace facebook account din su, kuma ake damfarar mutane da shi alhali shi wannan mutumin baisan hakan ba harsai ansanar da shi alabashin ya ษauki matakin dawo da facebook account ษin sa.
Shawara ga reku mutane, da ku daina sa lambar wayar ku a matsayin password ษin ku wai domin tafi sauฦin tunawa, ko kuma shekarar haihuwar ku, ta hakanne ake samun damar hacking - ฦwace Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauran su, accounts ษin ku. Sabida haka, ku riฦa following mu ta wannan page๐ Uncle Yunus
TANBAY: Wai shin me yasa mutane ke faษawa hannun waษannan ฦดan damfarar - 419?
✍️ Uncle Yunus
No comments:
Post a Comment